17 Mayu 2026 - 02:11
Source: ABNA24
Zanga-Zangar Adawa Da Sahayoniyawa Ta Mamaye Turai

Dubun dubatar mutane a duk faɗin Turai sun gudanar da zanga-zangar don tunawa da shekaru saba'in da takwas (78) na ranar Nakba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A Stockholm, jama'a masu yawa sun taru a dandalin Odensplan domin amsa kiran wasu kungiyoyin farar hula, suna neman a kawo karshen laifukan ta'addanci yaki na Isra'ila a Gaza.

A Athens, babban birnin Girka, masu zanga-zangar sun yi macci da tattaki zuwa ga ofisoshin jakadancin Isra'ila da Amurka.

A Paris, masu zanga-zangar kuma sun fito kan tituna don nuna goyon baya ga Falasdinawa.

A London, 'yan sanda sun fara wani babban aikin tsaro, kuma an gudanar da zanga-zanga da yawa a duk faɗin birnin.

.....................

Your Comment

You are replying to: .
captcha